Shugaban Tarayyar Jamus Horst Köhler ya fara kai wata ziyara a kasar Poland. | Labarai | DW | 18.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Tarayyar Jamus Horst Köhler ya fara kai wata ziyara a kasar Poland.

Shugaban tarayyar Jamus, Horst Köhler, ya isa a birnin Warsaw, na ƙasar Poland, inda zai halarci bikin buɗe wani taron baje kolin litattafai na ƙasa da ƙasa. Tuni dai shugaba Köhler ya gana da takwaran aikinsa na ƙasar Poland ɗin, Lech Kaczynski, inda dukkansu biyu suka yabi kyakyawar dangantakar da ke tsakanin ƙasashensu.

A cikin jawabin da ya yi wa taron maneman labarai bayan ganawar, shugaba Köhler ya ce duk da bambance-bambancen ra’ayoyin da ake samu a wasu lokutan, tsakanin Jamus da Poland, hulɗoɗin dangantakansu sai bunƙasa suke yi. Ya ƙara bayyana cewa:-

„Bari in yi amfani da wannan damar, wajen bayyana farin cikin ganin cewa, duk da bambance-bambancen ra’ayoyin da muke samu, a yunƙurin da ko wannenmu ke yi a nasa ɓangaren, wajen kyautata halin rayuwar al’ummominmu, ba ma bari irin wannan saɓanin ya janyo mana hauhawar tsamari tsakaninmu.“

Babbar matsalar da ke tsakanin ƙasashen biyu a halin yanzu dai ita ce, batun aikin shimfiɗa bututun man nan da Rasha da Jamus za su yi a ƙarƙashin tekun Baltic, wanda Poland ɗin ke nuna ɓacin ranta a kansa, saboda ganin da take yi kamar an yi mata saniyar ware ne a cikin wannan harkar.