1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Tanzaniya ya tsige wani Minista

Mouhamadou Awal BalarabeMay 21, 2016

Laifin shiga majalisar dokoki bayan shan barasa ya sa shugaban kasar Tanzaniya John Magufuli ya kori Ministan cikin gidan kasar Charles Kitwanga daga bakin aiki.

https://p.dw.com/p/1IsPT
Tansania Präsident John Magufuli
Hoto: Getty Images/AFP/D. Hayduk

Shugaba John Magufuli na Tanzaniya ya tsige ministan cikin gidan kasar daga mukaminsa, sakamakon bayyana da ya yi a buge a gaban majalisar dokokin kasar. Firaministan Tanzaniya Kassim Majaliwa wanda ya bayar da wannan sanarwa ta kafar talabijin, ya ce Minista Charles Kitwanga bai samu damar amsa tambayoyin 'yan majalisa ba saboda ya fita daga hayyacinsa sakamakon shan barasa. Sai dai ba a bayyana ranar da wannan lamari ya faru ba.

Da ma tun bayan da ya dare kan kujerar mulki a watan Oktoban 2015, shugaba Magufuli ya sha alwashin yakar rashin da'a tsakanin manyan jami'an gwamnatin Tanzaniya. Tuni dai shi shugaban da ake yi wa lakabi da "bulldozer" ya soke tafiye-tafiyen banza da wofi da liyafa da manyan jami'an gwamnati suka saba shiryawa.

Idan za a iya tunawa dai ,shugaban Tanzaniya ya soke bikin zagayowar samun 'yancin kai a watan Disemban bara, domin samun kudin yakar cutar Cholera da ta addabi kasar. Sannan a yanzu haka ya karkata kan ma'aikatan boge da ke karbar albashi ba tare da sauke nauyin da ya rataya musu a wuya ba.