1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Syria Bashar Al-Assad ya jinjinawa kungiyar Hizbullahi

August 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bumh

Shugaban kasar Syria Bashar Al-Assad, ya gabatar da jawabi mai zafi, wanda a cikin sa ya yi kaukyawan yabo, ga shugaban kungiyar Hezbollah Cheick Hassan Nasrallah, a sakamakon nasara da ya ce dakarun Chi á sun samu, a kan makiya bani yahudu, bayan fiye da wata guda a na gumurzu.

Al assad ya yi yabo ga saban yanayin da ke wakanan yanzu a gabas ta tsakiya, qwanda yayi daidai da bukatar da Syria.

Ya yi Allah wadai da manufofin Amurika da yan kazagin ta a wannan yanki.

Basahr Al Assad ya zargi Isra´ila da fakewa bayan sojojin ta 2, da aka kama domin kai farmaki ga kasar Labanon.

Shugaban ya ce ba boye ya ke ba Syria na bada tallafi ga Hezbollah kuma zata ci gaba da haka domin shine yayi daidai da bukatocin al´ummomin Syria.

Ya ce ba shi tsammanin za a samar da zaman lahia, cikin gagawa, domin bani yahudu makiya ne , kuma Syria zata ci gaba da daukar su a wannan matsayi.

Babu batun zaman lahia, muddun Isra´ila zata ci gaba da kasancewa shiriya, maida jikin wani na ki, ta hanyar mamaye kashen da ba halaliyar ta ba.

A ko da washe, sai ka ji wasu mutane na fadar cewa, Amurika na da muhimancin a fannin warware rikicin gabas ta tsakiya, amma wanan batu ba gaskiya bane. Amurika itace kanwa uwar gami , kazalika ita ke da alhakin rura wutar rikicin yanki, itace babbar mai adawa da zaman lahiaA daya hannun, Bashar Al Assad, ya zargi gwamnatin Labanon da zama karen farautar Isra´ila.

Jim kadan bayan wannan jawabi ministan harakokin Jamus Frank Walter Steinemeir, da ke ziyara a yankin gabas ta tsakiya, ya soke ganawa da hukumomin Syria.

A nata bangare gwamnatin Labanon ta fara shirye shiryen tantanawa, da zumar samar da masalaha,a game da batun makomar kungiyar Hezbollah, bayan aika rundunar shiga tsakanin ta Majalisar Dinkin Dunia.