1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Sudan yace zaiyi maraba da taimakon majalisar dinkin duniya

October 5, 2006
https://p.dw.com/p/BuhL

Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-bashir yace zai yi maraba da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ga dakarun kungiyar taraiyar Afrika dake aiki a yankin Darfur.

Sudan din dai ta shirya fuskantar kasashen duniya inda taki amincewa da kudirin komitin sulhu na MDD daya bukaci a ike da fiye da sojoji 20,000 na majalisar da zasu maye gurbin dakarun Afrika.

Sai dai al-Bashir yace zai yi maraba da duk wani taimako na kudi da kayan aiki da majalisar zata iya baiwa AU domin kawo karshen rikicin na Darfur wanda ya tilasatwa mutane fiye da miliyan 2 da rabi tserewa daga gidajensu.

Ministan harkokin wajen Sudan Lam Akol yace suna bukatar jamia 10 zuwa 20 da zasu taimakawa AU karkashin jagorancin AU din.

Yace abinda suke so shine karawa AU karfi domin ta gudanar da aiyukanta na wanzar da zaman lafiya.