Shugaban Sudan ya nuna amincewa da tallafin MDD
December 27, 2006Talla
Shugaban Sudan Omar al-Bashir ya ce ya amince da wani taimako na MDD da zumar kawo karshen rikicin yankin Darfur. A cikin wata wasika da ya aikewa babban sakataren MDD mai barin gado Kofi Annan, shugaba al-Bashir ya ce a shirye ya ke ya shiga tattaunawa don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta cikin gaggawa. Shirin MDD mai matakai guda 3 ya tanadi kara yawan dakarun kungiyar tarayyar Afirka su kimanin dubu 7 a Darfur. Kawo yanzu wadannan dakarun sun gaza wajen kwantar da kurar rikicin yankin da ke yammacin Sudan. To sai dai jami´an diplomasiya sun nunar da cewa har yanzu shugaba al-Bashir na adawa da girke dakarun MDD kasancewar ya janye daga dukkan yarjeniyoyin da aka kulla da shi a baya a dangane da yankin na Darfur.