1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Somalia ya yi amai ya lashe

May 20, 2010

Frime ministan Somalia ya koma bisa muƙamin sa bayan sallamar da shugaban ƙasar ya yi masa

https://p.dw.com/p/NTLH
Omar SharmarkeHoto: AP

A yau ne shugaban ƙasar Somalia Sharif Sheik Ahmed ya mayar da Frime Minista Omar Abdirrashid Sharmarke a muƙamin sa bayan da aka sauke shi a makon da wuce sakamakon ƙuri'ar rashin amincewa da jagorancin sa da majalisar dokokin ƙasar ta kaɗa.

'Yan majalisa 280 ne suka kaɗa kuri'ar da ta sa aka sauke Shamarke da ministocin sa amma duk da haka Frime Ministan ya ce, bai sauku ba saboda bai yarda da hukuncin da shugaban ƙasar ya yanke ba.

Shugaba Sharif Sheikh Ahmed ya faɗa wa manema labarai cewa ya mayar da sharmarke a muƙamin sa ne bayan da ya tuntuɓi lauyoyin sa waɗanda suka shaida masa cewa hukuncin da ya yanke ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar.

Tun watan disambar bara ne rabon majalisar dokokin Somalia yin wata zama sakamakon rashin tsaro da yaƙe-yaƙen da ƙasar ke fama da su lamarin daya sa 'yan majalisar suka koma suna zama a ƙasashen ƙetare.

Rigingimun da Somalia ke fama da su dai sun haɗa da 'yan fashi akan Tekun Aden, wanda ya haɗe Turai da Asiya da kuma Afirka, matsalar da kuma a yanzu ƙasashen duniya ke ƙoƙarin shawo kanta.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Ahmad Tijani Lawal