Shugaban Rasha ya soki lamirin ƙasashen yammacin duniya | Labarai | DW | 22.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Rasha ya soki lamirin ƙasashen yammacin duniya

Shugaban ƙasar Rasha Vladmir Putin ya zargi ƙasashen yammacin duniya da tsoma baki cikin harkokin siyasar ƙasarsa.Wajen wani gangami da siyasa a birnin Moscow shugaban na Rasha yace gwamnatocin ƙasashen ketare suna ɗaukar nauyin abokan adawarsa durkusar da ƙasar ta Rasha don su samu damar aiwatar da abinda ya kira ƙazaman dabarunsu.Wannan tsauraran kalami na Putin ya zo ne wata guda kafin zaɓen majalisar dokokin ta Duma.Putin dai shi ke kan gaba cikin jerin `yan takara na jamiyar United Russia wadda take gaba a kuriar jin raayin jama`a da aka gudanar a ƙasar.