1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Poland ya rasu a hatsarin jirgin sama

April 10, 2010

Hatsarin jirgin sama ya janyo mutuwar shugaba Kaczynski da manyan jami'an ƙasar Poland

https://p.dw.com/p/Msgo
Marigayi shugaba Kaczynski na Poland da Uwargidarsa MariaHoto: AP

Shugaban ƙasar Poland Lech Kczynski, tare da wasu manyan jami'an gwamnatin ƙasar sa sun rasu a wani hatsarin da jirgin shugaban ƙasar ya yi - dai dai lokacin da yake shirin sauka a filin jirgin samar garin Smolensk dake ƙasar Rasha. Jami'an kwana - kwana suka ce babu wanda ya tsira da ransa daga cikin ɗaukacin waɗanda ke cikin jirgin - ƙirar Tupolev, mai ɗaukar fasinjoji 154, wanda kuma Rasha ce ta ƙera, kana yake ɗauke da mutane 96 ciki harda Uwargidar shugaban Poland ɗin. Jami'an gwamnatin Poland ɗin na kan hanyar su ce ta zuwa yankin Katyn dake kusa da garin Smolensk domin halartar shagulgular cika shekaru 70 na tunawa da kissar da tarayyar Soviet ta yiwa fiye da mutane dubu 20 na jami'ai da kuma ƙwararrun ƙasar Poland a lokacin yaƙin Duniya na biyu.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce ta yi matuƙar kaɗuwa da jin labarin mutuwar shugaban na Polan Kaczynski, a yayin da ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle kuwa ya bayyana cewar, lallai Poland ta sami kanta cikin yanayin jimami.

A halin da ake ciki kuma, Frime Ministan ƙasar ta Poland Donald Tusk na kan hanyar sa ta zuwa yankin da hatsarin ya faru, kuma ya bayyana cewar, majalisar zartarwar ƙasar za ta gudanar da wata zama - da zarar ya dawo can an jima da yamma.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Muhammad Nasir Auwal