Shugaban Palasdinawa yayi maraba da rahoton Baker | Labarai | DW | 06.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Palasdinawa yayi maraba da rahoton Baker

Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas yayi maraba da rahotan da hukumar da Amurka ta nada kann Iraki ta gabatar ,wanda ke kira ga shugaba George W Bush daya sake farfado da daftarin samarda da zaman lafiya da akayi watsi dashi,a yankin gabas ta tsakiya.Kakakin shugaban Palasdinawan Nabil Abu Rudeina ya fadawa kamfanin dillancin labaru na AFP cewa ,rahotan yayi nazarin ababai muhimmai.Yace babu shakka warware matasalar palasdinawa,zai bude kafar warware dukkan rigingimu na yankin gabas ta tsakiya.Shima kakakin Kungiyar Hamas,wadda Amurka ta sanya a jerin kungiyoyin yan tarzoma Fawzi Barhum,yace dafatan yan siyasar Amurkan a wannan karon zasuyi koyi da darasin dake kunshe a wannan rahoto,tare da sanin cewa manufofinsu basu haifar da da mai idanu ba.