1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban NATO a Afghanistan ya gana da Pervez Musharaf

Shugaban rundunar tsaro ta NATO, a ƙasar Afghanistan Jannar David Richards, ya tantanna yau, da shugaban ƙasar Pakistan Pervez Musharaf.

An yi wannan ganawa, a daidai lokacin da, a ke zargin jami´an leƙen asirin Pakistan, da nuna haɗin kai ga mayaƙan Taliban.

Jim kaɗan kamin taron, Jannar Richards, ya ƙaryata raɗe- raɗin da ake, na cewar ya zo ne, domin ya nunawa Pervez Musharaf, hujjojin da ke tabbatar da goya bayan da jami´na sa, ke baiwa yan Taliban.

Ya ce maƙasudin wannan ziyara, na da nasaba, da ciwo kan hukumomin Pakistan, su ƙara bada haɗin kai, ga ƙoƙarin NATO, na samar da zaman lahia a yankin.

Rundunar tsaro ta NATO, ta shiga wani hali, na tsaka mai wuya, tun bayan da ta ɗauki jagorancin sojojin ƙasa da ƙasa a Afghanistan.

Tun shekara ta 2001, da sojojin Amurika, su ka kori dakarun Taliban daga kujera mulki, a Afghanistan, shekara bana, na matsayin ƙoluluwar tashe-tashen hankulla a wannan ƙasa.

Daga watan Janairu, zuwa yanzu ,a ƙalla mutane 2.500 su ka rasa rayuka, da su ka haɗa da sojojin ƙetare 140.