Shugaban Najeriya ya zaɓi mataimakin sa | Labarai | DW | 13.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Najeriya ya zaɓi mataimakin sa

Shugaba Goodluck Jonathan ya zaɓi gwamnan Kaduna domin zama mataimakin shugaban ƙasa

default

Shugaban Najeriya Jonathan Goodluck

Rahotanni dake fitowa daga Najeriya na cewar shugaba Goodluck Jonathan ya zaɓi gwamnan Jihar Kaduna Namadi Sambo domin zama mataimakin shugaban ƙasa. A yau shugaban ƙasar zai aike da sunan gwamnan na Kaduna dake arewacin Najeriya zuwa gaban Majalisun dokokin ƙasar domin samun amincewar su.

A waje ɗaya kuma wani maitaimakawa shugaban Najeriya Goodluck Jonathan akan harkokin majalisar dokoki ya shedawa kanfanin dillancin Labaran Reuters cewar akwai alamun shugaba Goodluck Jonathan ya tsaya takarar zaɓen shekara ta 2011.

Cairo Ojuogboh ya shedawa manema labarai cewar shugaban zai nemi tsayawa takarar muƙamin shugaban ƙasa a zaɓen shekara ta 2011 a ƙarƙashin tutar jam'iyar PDP, duk kuwa da tsarin da Jam'iyar tace tanabi na karɓa-karɓa tsakanin ɓagarorin  ƙasar huɗu.

Koda yake tuni kakakin shugaban Goodluck Ima Niboro yace wancan jami'i bashi da ikon magana dayawun shugaban ƙasar, tun kafin rasuwar shugaba Umaru Musa Yar'adua ne dai jam'iyar dama sauran al'umar ƙasar suka raba kawunan su akan batun tsayawa takaran shugaba Goodluck Jonathan. A lokacin wata ziyara daya kai Amirka, shugaba Jonathan yace dokar ƙasa ta bashi damar tsayawa takarar.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Umaru Aliyu