Shugaban Najeriya ya koma gida | BATUTUWA | DW | 10.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Shugaban Najeriya ya koma gida

Bayan doguwar jinya a kasar Birtaniya Shugaba Muhammadu Buhari na Tarayyar Najeriya ya koma gida.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar ya koma gida ne da safiyar wannan Jumma'a, bayan shafe kimanin wata guda da rabi ana duba lafiyarsa a birnin London na kasar Birtaniya. Babu karin haske kan lafiyar shugaban. Ranar 19 ga watan Janairun wannan shekara da muke ciki ta 2017 ne, Shugaba Buhari ya yi balaguro zuwa Ingila domin duba lafiyar tasa. Shugaban ya sauka ne a filin jirgin saman sojoji da ke Kaduna sakamakon rufe na Abuja, saboda gyara da za a yi a kan hanyar da jiragen sama ke sauka.