1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Buhari ya karrama Abiola

June 12, 2018

A ranar 12 ga watan Yuni, shugaba Muhammadu Buhari na Tarayyar Najeriya ya karrama marigayi Cif MKO Abiola da lambar girma mafi daraja a kasar tare da neman gafarar iyalan Abiolan.

https://p.dw.com/p/2zOyE
Regimegegner Nigeria Chief Moshood Abiola
Marigayi MKO Abiola na NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa

An karanto tarihin marigayi Cif  Abiola wajen wani bikin karrama zaben na 12 ga watan Yuni da a ka soke shekaru 25 da suka gabat, duk da cewa a wancan lokacin an yi yakinin shi ya lashe zaben. Shugaban kasar Muhammad Buhari dai ya karrama Abiolan da lambar girma mafi daraja a kasar a wajen bikin da ke kama da na siyasa amma kuma ya samu halartar daukacin magoya bayan fafutukar zaben na wancan lokaci. Buhari ya tabbatar da nasarar zaben da Abiola ya lashe amman kuma gwamnatin soja a wancan lokacin ta soke. Shugaban na Najeriya ya nemi afuwar iyalan marigayi Cif MKO Abiolan da ma daruruwan mutanen da suka rasa rayukansu a yayin fafutukar.

 

Yafiya daga iyalan marigayin

Schauspiel Seven Brüssel Belgien
Hafsat Abiola ta farko daga haguHoto: DW/C. Stefanescu

Tsallen murna dai na zaman karatu na magoya bayan Abiolan dama 'ya'yan tsofaffin jam'iyyar SDP da ke kallon ranar ta musamman ga kokari na dinkewar kasa dama yafiya a tsakanin juna. Haka zalika suma iyalai na Abiola sun ce sun yafe tare da neman afuwar kowa a kokari na sassantawa, inji diyar marigayin da ta wakilici iyalan Hafsat Abiola Costello. Abun jira a gani dai na zaman tasirin sasantawar a cikin burin sake tabbatar da samun kuri'ar ta Kudu maso Yamma da ke zaman mai tasiri a zabukan da ke tafe.