Shugaban Najeriya ya bada umurnin karbo turawa da akayi garkuwa da su | Labarai | DW | 17.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Najeriya ya bada umurnin karbo turawa da akayi garkuwa da su

Shugaban Najeriya Chief OBJ ya baiwa jamian tsaro umurnin ganin sunci nasarar karbo turawa 4 da akayi garkuwa da su,bayan mako guda na tabarbarewar alamura a harkokin mai a Najeriyar,kasa ta shida mafi girma daga cikin kasashen da suke samarda man fetur a duniya.

Cikin wani taron gaggawa da yayi da manyan yan siyasa da shugabannin soji,Obasanjo,ya kafa wata tawaga da zata yi kokarin ganin an sako mutanen 4,yan kasashen Amurka,Burtaniya Bulgaria da Honduras da aka sace kwanaki shida da suka shige.

A ranar 11 ga wannan wata ne,wasu yan bindiga suka sace wadannan turawa,suna masu bukatar a sako shugabanninsu guda biyu.Shugabannin nasu kuwa sune, Mujahid Dokubo Asari,wanda ke fuskantar laifin yiwa kasa zagon kasa da kuma tsohon gwamnan jihar Bayelsa da aka tsige bisa laifin halatta kudin haram da cin amanar kasa.

Bayan sace wadannan mutane yan tawayen na Ijaw sun kuma fasa bututun mai a ranar lahadi,wanda ya janyowa najeriya hasarar ganga 211,000 a kowace rana tare da tsawwala farashin mai a kasuwannin duniya,mafi tsanani cikin watanni 3.