Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dawo gida | BATUTUWA | DW | 10.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dawo gida

Bayan share watanni biyu na jinya a London, shugaban Najeriya ya dawo Abuja bayan da jirgin da ya daukoshi ya sauka a filin jirgin saman Kaduna. An yi ta kace-nace dangane da dadewa da Buhari ya yi a ketare.

Muhammadu Buhari steigt aus einem Flugzeug (GettyImages/AFP/M. Safodien)

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dawo gida

 A cikin  raha da tsallen murna da ma farin ciki  ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya gudanar da ganawarsa ta farko da ministoci da manyan hafsoshi na tsaro dama gwamnoni a wajen wani dan karamin biki na tarbonsa. Shugaban da ya bar kasar tun daga ranar 19 ga watan Janairun da ya shude dai, ya dawo birnin Abuja da alamun karfi, sannan kuma a cikin fatan gyaran kasa da ya sa wa gaba.

Shugaba Buhari ya yi godiya ga 'yan Najeriya

Mohammadu Buhari (picture-alliance/epa/Stringer)

Shugaba Muhammadu Buhari ya godewa 'yan Najeriya

Bulagurun na Buhari da ke zaman irinsa mafi dadewa tun bayan hawansa mulki na kasar watanni 20 da doriya dai ya haifar da kace nace cikin kasar a tsakanin masu tunanin an boye gaskiyar halin lafiya ta shugaban. Abun kuma da ya sa dawowarsa Abujar ta kwantar da hankula tare da sabon fatan kai karshen kiki-kakar da ke iya kaiwa ga kassara lamura. A wani kwarya-kwaryar jawabi ga 'yan kasar dai shugaban ya ce ya shirya tsaf domin dorawa a cikin aikin da a cewarsa yake da karfin yi sosai.

Su ma mabiya da jami'ai na gwamnati dai na murnar har kune da ganin dawowar shugaban. Kama daga ministocinsa har ma da wasu gwamnonin jihohin kasar irinsu gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje na Kano da ke zama daya daga cikin gwamnonin da suka zo domin yi masa barka da dawowa.

Jama'a sun nuna farin ciki da isowar Buhari

Afrika Nigeria - Präsident Muhammadu Buhari (Reuters/Stringer)

Shugaba Buhari ya sauka a filin jirgin saman sojoji na Kaduna

Shi kansa babban sufeto Janar na 'yan sanda na Tarayyar ta Najeriya dai ya ce ya gamsu da abun da 'ya kalla daga shugaban da ya raka a kan hanyar birnin London sannan kuma ya tarbeshi da safiyar Jumma'a a Abuja. Sai dai duk da cewar ya dawo da alamar rama, ana sa ran shugaban zai kama aiki gadan-gadan tun daga Litinin da ke tafe.

Sauti da bidiyo akan labarin