Shugaban Mali ya baiyana aniyarsa ta tsayawa takara | Labarai | DW | 27.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Mali ya baiyana aniyarsa ta tsayawa takara

Shugaba Ahmadou Toumani Toure na kasar Mali ya baiyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a zaben shugaban kasa da zaa gudanar a wata mai zuwa.

Kanfanin dillancin labaru na AFP ya baiyana cewa tuni dai wasu yan takara 8 suka baiyana aniyarsu cikinsu har da kakakin majalisa tsohon firaminista Ibrahim Boubakar Keita.

A ranar 29 ga watan afrilu aka shirya zaa gudanar da zagayen farko na zaben zai kuma a ranar 13 ga watan maris zaa yi zagaye na biyu tsakanin yan takara biyu da suka kann gaba idan baa samu wanda ya lashe zaben ba.

Toure wanda tsohon janar ne na soji,ana yabonsa da kokarin fidda kasar mali daga mulkin kama karya na soji karkashin Moussa Toure,yana mai maida kasar tafarkin demokradiya.

Shine kuma ya jagoranci shirin mika mulkin a 2001 kafin ya lashe zaben shugaban kasar.