Shugaban Madagascar ya sake lashe zabe
December 10, 2006Talla
Shugaban kasar Madagascar Marc Ravalomanana ya sake samun nasarar ci gaba da mulki na karin shekaru 5 a kasar bayan zabe da aka gudanar.
Rahotanni daga maaikatar harkokin cikin gida ta kasar sunce Ravalomanana ya samu lashe kashi 58 da digo 8 cikin dari na kuriu da aka kada a zaben na makon daya gabata,inda kashi 61 na jamaar kasar miliyan 7 suka jefa kuriarsu.