Shugaban Kazakhstan ya lashe zaben kasar | Labarai | DW | 05.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Kazakhstan ya lashe zaben kasar

Shugaba Nursultan Nazarbayev,wanda yake mulkin kasar Kazakhstan tun a karkashin tsohuwar taraiyar soviet,ya sake lashe zaben shugaban kasar da gagarumin rinjaye.

Hukumar zabe ta kasar tace shugaban ya lashe zaben da kashi 91 cikin dari na kuriu da aka kada a zaben na jiya lahadi.

Abokin hamaiyarsa ya samu damar samun kusan kashi 7 na kuriun.

Tuni dai abokan dawa sun fara korafin cewa gwamnati bata bada damar yan adawa sun jefa kuria ba.

Ana su bangare jamian gwamnatin sun fara zargin yan adawa da shirin gudanar da zanga zanga irin wadanda suka gudana a kasashen Georgia,Ukraine da Kyrgistan,cikin shekaru biyu da suka shige,wanda ya taimaka yan adawa suka kwaci ragamar mulkin kasashen