Shugaban kasar Sudan ya tabbatar da goyon bayansa ga shirin zaman lafiya na Darfur | Labarai | DW | 26.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban kasar Sudan ya tabbatar da goyon bayansa ga shirin zaman lafiya na Darfur

Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir ya tabbatar da goyon bayansa ga shirin zaman lafiya da ya kunshi aikewa da dakarun MDD da AU zuwa yankin Darfur.

Cikin wata takarda daya aikewa sakatare janar mai barin gado Kofi Annan al-Bashir ya baiyana shirin gwamnatinsa da fara aiwatar da shirin ba tare da bata lokaci ba kamar dai yadda aka tsara wajen tarukan AU a kasashen Ethiopia da Abujan Najeriya.

Wani kakakin AU a birnin Khartoum yace kashin farko na masu bada shawara na MDD zasu kama hanyarsu ta zuwa Darfur cikin wannan mako domin taimakawa a dakarun AU dake lardin na Darfur.