1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban kasar Sudan ya jinjinawa kungiyar Hizbullahi

Shugaban kasar Sudan Omar El Beshir, ya ce dakarun Sudan, a shire su ke, su yaki sojojin Majalisar Dinkin Dunia, a yankin Darfur, kamar yadda Hezbollah ta gasa aya a hannun rundunar isra´ila a yakin da su ka gwabza tsawan kwanaki 34.

Shugaba En Bashir yayi wannan jawabi yau talata a garin Jebel Awlia, da ke tazazara kilomita 50 da birnin Khartum, albarakacin ciwkan shekaru 52, da girka rundunar tsaro ta kasa.

Omar El Bashir, ya yi yabo da jinjinna damtse, ga shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah, a sakamakon jan na mijin kokari, da kwazon da ya nuna, ta fannin fatattakar dakarun Isra´ila a kudancin Labanon.

Gwamnatin Sudan na ciu gaba da nuna adawa ga matakin da Majalisar Dinkin Dunia ke bukatar dauka, na aika dakarun shiga tsakani dubu 19, a yankin Darfur da ke fama da rikicin tawaye.

A ziyara da ya kai makon da ya gabata a Darfur, sakataran hukumar bada agaji ta Majalisar Dinkin Dunia, Jan Egeland, ya tabbatar da cewa, akwai bukatar aika rundunar a yankin ta la´akari da ukubar da al´ummomi ke fuskanta daga bangarori daban-daban na yan tawaye da kuma dakarun gwamnti.