Shugaban kasar Kenya ya yi wa Gwamnati garambawul | Labarai | DW | 14.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban kasar Kenya ya yi wa Gwamnati garambawul

Shugaban kasar Kenya Maw Kibaki, ya yi garambawul ga gwamnatin kasar.

Ya nada wasu sabin ministoci 3, domin maye gurbin ministocin da su ka yi murabus, a sakamakon tuhumar su da ake, da hannu, a cikin al´ammuran ci hanci da rashawa .

Wannan ministoci, sun yi murabus a farkon watan da mu ke ciki, domin amsa tambayoyin kotuna, a game da zargin da a ke masu, na karbar rashawa ta maggudan kudade.