1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban kasar Kenya ya rusa gwamnatin sa

November 23, 2005
https://p.dw.com/p/BvJm

Shugaban kasar Kenya Maw Kibaki, ya russa gwamnatin sa, bayan mummunan kayin da ya sha, a zaben jin ra´ayi jama´a, a game da kundin tsarin mulkin kasa, da a ka gudanar ranar litinin da ta wuce.

A jawabi da yayi ta kafofin sadarwa, ya nunar da cewa, bayan abunda ya wakana, ya zama wajibi a gare sa, ya yi garambawul ga gwamnati kasancewar an samu rabuwar kanu tsakanin ministoci lokacin yakin neman zabe.

A yayin da wasu su ka yi kampe ta rashin amicewa da kundin tsarin mulkin, wasun kuwa sun bukaci a amince da shi.

Shugaban ya sannar da cewa, nan da sati 2 masu zuwa, zai kafa wata sabuwar gwamnati, da za ta dukkufa ga ayyukan ci gaban kasa.

Masharahanta na hasashen cewa, a cikin sabuwar gwamnatin da za a girka sahugaban zai fidda dukkan ministocin da su ka kiri al´umma da ta kauracewa kundin tsarin mulkin.