1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban kasar Jamus ya isa Madagaskar

April 7, 2006

A zangonsa na biyu a ziyararsa ga kasashen Afurka shugaban kasar Jamus Horst Köhler ya gana da shuagabannin Madagaskar

https://p.dw.com/p/Bu0l
Köhler da Ravalomanana
Köhler da RavalomananaHoto: picture-alliance / dpa/dpaweb

Shugaban kasa Horst Köhler, wanda a matsayinsa na darektan asusun ba da lamuni na IMF ya kai ziyara kasar Madagaskar a shekara ta 2003 domin ganawa da shugaba mai ci Marc Ravalomanana ya yaba da kyakkyawar niyyar dake tattare da shuagabannin kasar a game da canza manufofinta a lokacin wani taron manema labaran da ya gudanar a Antananarivo fadar mulkinta. Köhler ya ce kasar ta samu ci gaba matuka ainun tun bayan waccan ziyara da ya kai. Köhler ya kara da cewar:

“Wani abin da na lura da shi a nan kasar tun bayan ziyarata a shekara ta 2003, shi ne kasancewar kasar Madagaskar ta samu gagarumin ci gaba akan wannan hanya madaidaiciyar da take akai domin samar da bunkasar tattalin arziki da kayyade matsalar talauci tsakanin al’umarta.”

Shugaba Marc Ravalomanana yana bin tsauraran matakai na garambawul ga tattalin arzikin Madagaskar. Amma masu sukan lamirin manufofinsa na korafin cewar yana tafiyar da al’amuran kasar kamar dai wani kamfani ne dake karkashin shugabancinsa. Amma bisa ga ra’ayin shugaban kasar Jamus Horst Köhler wani abin da zai zama mizanin auna ci gaban da kasar ta samu a matakanta na garambawul shi ne zaben shugaban kasa da za a yi shekara mai zuwa. Shi dai shugaba mai ci Marc Ravalomanana ya ba da tabbacin cewar MDD ce zata dauki alhakin sa ido a matakan shirye-shiryen zaben ko da yake ya hakikance cewar har yau da sauran rina a gaba a fafutukar da kasar ke yi na tabbatar da mulkin demokradiyya da aikin doka. Madagaskar na bukatar taimako daga ketare domin cimma burinta in ji shi. Wannan maganar sai da aka tabo ta a ganawa tsakaninsa da Köhler, kamar yadda shugaban na Jamus ya nunar ya kuma kara da bayanin cewar:

“Na yi matukar murna da farin ciki a game da daidaton bakin da muka samu a game da cewar salon kamun ludayin gwamnatin Madagaskar shi ne zai bude hanya ga ‘yan kasuwar Jamus da na sauran kasashen ketare wajen zuba jari a wannan kasa.”

Tun abin da ya kama daga shekara ta 1960 Jamus ke ba da tallafi ga kasar Madagaskar, inda ta kebe tsabar kudi Euro miliyan 15 da dubu dari biyar na taimako ga kasar tsakanin shekara ta 2005 da ta 2006. Ana amfani da wadannan kudade ne wajen kare kewayen dan-Adam da dakatar da yaduwar cutar kanjamau tare da ba da goyan baya ga shugabanci na gari a wannan kasa.