1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban kasar Jamus ya gana da wakilan majalisar dokoki

June 21, 2005

A yau talata shugaban kasar Jamus Horst Köhler ya sadu da wakilan majalisar dokoki domin neman haske a game da yiwuwar gudanar da sabon zabe a kasar

https://p.dw.com/p/BvbC
Shugaban kasar Jamus Horst Köhler
Shugaban kasar Jamus Horst KöhlerHoto: AP

Manazarta al’amuran yau da kullum dai sun yi nuni da cewar shugaban kasa Horst Köhler na da cikakken ikon rushe majalisar dokokin, amma ba lalle ba ne yayi hakan. Kazalika yana da ikon tilasta wa shugaban gwamnatin da a halin yanzu ba ya da sauran amanna, domin ci gaba da tafiyar da al’amuran mulki har zuwa karshen wa’adin mulkinsa, ko kuma ya sa ido ya ga ko shin ita kanta majalisar dokokin zata tsayar da wata shawarar zaben wani sabon shugaban gwamnatin. Idan har shugaban gwamnati ya tsayar da shawarar yin murabus daga mukaminsa, a nasa bangaren shugaban kasa na da ikon gabatar da shawara akan wasu sabbin ‚yan takara domin mayewa gurbinsa. A sakamakon haka ne shugaban kasa yake sara yana mai duban bakin gatari dangane da shawarar da zai tsayar akan mawuyacin halin da ake ciki yanzu haka a siyasar Jamus. Horst Köhler ya gudanar da shawarwari tare da kwararrun masana al’amuran doka da jami’an siyasa, abin da ya hada har da Roman Herzog, tsofon shugaban kasar Jamus kuma alkalin alkalai a kotun koli ta kasar. Bayanai da Herzog ya bayar a game da daftarin tsarin mulkin na tabbatar da cikakkiyar damar da shugaban kasa ke da shi dangane da shawarar da zai iya tsayarwa, a yayinda ita kuma kotun kolin zata rika bin diddigin rawar da yake takawa akan manufa. A shekarar 1983 kotun kolin ta yanke hukuncin cewar shugaban kasa na da ikon rushe majalisar dokoki, idan har aka samu rinjayen kuri’ar rashin amanna da salon kamun ludayin shugaban gwamnati. Akan gudanar da irin wannan kuri’ar ce idan gwamnati mai ci na da kuma ‚yan hamayya sha’awar ganin an gudanar da wani sabon zabe, idan kuma ya kasance hakan ne kawai zai taimaka a fitar da kasa daga mawuyacin halin da take ciki. Domin neman haske a game da hakan ne shugaban kasa Horst Köhler ya nemi ganawa da jami’an siyasar dake da wakilci a majalisar dokoki ta Bundestag a yau talata. Abin da yake neman sani shi ne, ko shin lalle suna sha’awar ganin an gudanar da sabon zabe, da kuma matsayin gwamnati wajen tafiyar da al’amuran mulki ta la’akari da rinjayen da ‚yan hamayya ke da shi a majalisar gwamnonin jiha. A baya ga haka shugaban kasa Horst Köhler na so ya samu karin haske a game da matsayin dangantakar jam’iyyun SPD da The Greens dake hadin guiwa a gwamnati. A ganin shugaban dai a wannan bangaren ana fama da wasu manufofi na ci da ceto, wadanda ke taimakawa wajen tabarbarewar al’amuran mulkinsu na hadin guiwa.