shugaban kasar Jamus Köhler a Poland | Siyasa | DW | 31.08.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

shugaban kasar Jamus Köhler a Poland

A ganawar da suka yi da shuagabannin kasar Poland Köhler ya yaba da irin ci gaban da ake samu a dangantakarta da Jamus

Köhler da Kwasniewski

Köhler da Kwasniewski

A lokacin da suka gana da shugaba Aleksander Kwasniewski dake karbar bakuncin Köhler, dukkan sassan biyu sun yaba da kakkarfar alakar dake akwai tsakanin Poland da Jamus. Suka ce an samu ci gaba matuka ainun a kokarin da ake yi na dinke dukkan baraka da rashin jituwar da ta wanzu tsakanin kasashen biyu, wadanda a yanzu suke hadin kai domin bin wata manufa bai daya a kungiyar Tarayyar Turai. An saurara daga bakin Kwasniewski yana mai bayanin cewar:

A matsayina na shugaban kasa ina iya tabbatar muku da cewar an samu kyakkyawan ci gaba a dangantaka tsakanin Jamus da Poland. Kazalika zan yi amfani da wannan damar domin mika godiya ta ga Jamus dangane da goyan baya da kasar ta ba mu akan hanyarmu da ta fara da yaje-yajen aiki karkashin tutar kungiyar Solidarity, wacce ta taimaka aka samu tsattsauran canji ga yankin da nahiyar Turai da ma duniya baki daya, lamarin da a karshe ya kai ga sake hadewar kasar Jamus.

Sai dai kuma ko da yake a bangare guda shugaban na kasar Poland ya fito fili yana yabon rawar da Jamus ta taka dangane da kungiyar Solidarity, amma a daya bangaren Kwasniewski ya fito fili yana mai tofin Allah tsine da shirin gwamnatin kasar na bude wata cibiyar adawa da manufiofin fatattakar mutane daga yankunansu, a birnin Berlin. A ganinsa mai yiwuwa wasu su nemi yin amfani da wannan cibiya. A nasa bangaren shugaban kasar Jamus Horst Köhler yayi nuni da cewar wannan manufa ta bude cibiyar tana da magoya baya da kuma masu adawa da ita a saboda haka ya zama wajibi a gudanar da muhawara kanta tsakani da Allah:

Wani abin lura a nan shi ne kasancewar a hakika babu wata kafa ta siyasa a Jamus dake da niyyar amfani da wannan cibiya ko wani ra’ayi daban domin ba wa tarihi wata fassara ta dabam. Dukkan Jamusawa na sane da cewar kasarsu ce ke da alhakin ta’asa ta farko da ta kai ga yakin duniya na biyu.

Shugaban kasa Horst Köhler dai ya bayyanar a fili cewar zaman lafiya da cude-ni-in-cude-ka ba zai samu ba sai idan hulda ta kasance tsakani da Allah da kuma fahimtar gaskiyar cewar sai tare da musayar yawu tsakanin illahirin kasashen Turai ne za a samu sahihiyar fassara ga ma’anar guje-gujen hijira da fatattakar mutane daga yankunansu na asali. Daga wannan bayanin na Köhler jami’an Poland suka fahimci cewar shugaban kasar daga Jamus na ba da fifiko ne ga wata manufa ta hadin kai tsakanin kasashen Turai domin adawa da manufofin fatattakar mutane daga yankunansu na asali, bisa sabanin yadda lamarin yake dangane da Angela Merkel ‚yar takarar jam’iyyun Christian Union a zaben majalisar dokoki da shugaban gwamnati da za a yi a ranar 18 ga watan satumba.