1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban kasar Jamus Horst Köhler ya kammala ziyararsa ga Poland

September 1, 2005

Shugaban kasar Jamus Horst Köhler, a yau alhamis, ya kammala ziyararsa ta yini uku ga kasar Poland

https://p.dw.com/p/Bva1
Horst Köhler a Warsaw
Horst Köhler a WarsawHoto: AP

Horst Köhler, shi ne shugaban kasar Jamus na biyu da ya halarci irin wannan biki na zaman juyayi a kasar Poland, bayan magabacinsa Johannes Rau. Manufarsa game da halartar bikin shi ne domin nunarwa a fili cewar Jamus na sane da ummal’aba’isin yakin duniya na biyu, inda yake cewar:

Al’umar kasar Poland sun fuskanci ta’asa da danniya tsawon shekaru da dama bayan farmakin da aka kai kann kasar misalin shekaru 66 da suka wuce. Duniya gaba daya da shiga fama da wahala da barna iri-iri kana daga bisani kaikayi ya koma kann mashekiya saboda masifar yakin ya dawo kann ita kanta Jamus da halaka da yawa daga al’umarta da ba su san hawa ba ba su san sauka ba.

Shugaba Köler da takwaransa Kwasniewski sun shirya ganawa da ‚yan wata makaranta sakandare dake amfani dake amfani da harsunan Jamusanci da Polnisanci wajen koyarwa, domin bayyana hadin kann dake tsakanin kasashen biyu a kokarin kyautata makomar nahiyar Turai. A dai halin da ake ciki yanzu, kamar yadda shugaba Kwasniewski ya nunar, sama da matasa na kasar Poland miyan biyu da rabi ne ke koyan harshen Jamusanci, wanda wannan wata alama ce dake nuna azamar da kasar tayi wajen gina wata hadaddiyar nahiyar Turai. A nasa bangaren shugaba Horst Köhler ya bayyana farin cikinsa game da jin haka da kuma tahakikanin gaskiyar cewar kasar Poland ta fi Jamus yawan dalibai na gaba da sakandare yanzu haka, inda ya ce hakan na mai yin nuni ne da yadda kasar ta durfafi wata kyakkyawar hanya madaidaiciya domin yada ilimi da fasaha tsakanin al’umarta. Wannan wani muhimmin jari ne aka zuba, wanda kuma za a ci ribarsa nan gaba. A karshe shugaba Horst Köhler yayi wa matasan alkawarin kara fadada ayyukan hadin kai da musayar matasa tsakanin Jamus da kasar Poland, inda ya ce saboda su ne manyan gobe kuma makomar nahiyar Turai tana hannunsu.