1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Kasar Jamus A Benin

December 13, 2004

A ranar asabar da ta wuce shugaban kasar Jamus Horst Köhler ya isa Cotonou ta kasar Benin a matakin farko ga ziyararsa ga kasashen Afurka

https://p.dw.com/p/BveE
Shugaban Kasar Jamus Horst Köhler
Shugaban Kasar Jamus Horst KöhlerHoto: dpa

Jim kadan bayan saukarsa a Benin shugaban kasar Jamus Horst Köhler ya nanata kira ga kasashen gamayyar G7 da suka fi ci gaban masana’antu a duniya da su yi wa Allah da Ma’aiki su kara karfafa manufofinsu na yaki da matsalar talauci. Ya ce wadannan manufofi sun hada da kawar da shingen ciniki da kuma cika alkawarinsu na bunkasa yawan kudaden taimakon raya kasashe masu tasowa. A lokaci guda shugaban na kasar Jamus ya kara da yin tsokaci ga muhimmancin dake akwai na yunkurar kasashe masu tasowan domin taimakon kansu da kansu, sai ya kara da cewar:

Sanin kowa ne cewar kayan ado ba ya ado, kuma a saboda haka duk wani bakon ra’ayin da za a shigar da shi a nahiyar Afurka ba zai kai ga biyan bukata ba. Su kansu al’umar nahiyar ne ya kamata su tashi tsaye wajen farfado da tattalin arzikinsu. Tilas ne su yakin cin hanci da nuna son kai, in kuwa ba haka ba, za a wayi gari dangantakar taimakon raya kasa ba ta da wani amfani akan manufa. Dukkanmu dai jirgi daya ne ke dauke da mu a saboda haka nahiyar Turai ba zata samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma yalwa mai dorewa ba, sai fa idan ita ma nahiyar Afurka ta samu irin wannan dama daidai-wa-daida.

Ita dai kasar Benin tana daya daga cikin kasashen da Jamus ke ba su fifiklo a manufofinta na taimakon raya kasa, inda a cikin shekaru 40 da suka wuce kasar ta yammacin Afurka ta samu taimakon tsabar kudi na Euro miliyan 315 daga Jamus domin raya yankunanta na karkara da samar da ruwan sha mai tsafta ga jama’a da kare kewayen dan-Adam da kuma kyautata makomar albarkatun kasa da Allah Ya fuwace mata. A ziyarar tasa ga Benin shugaban kasa Hosrt Köhler, kazalika ya gana ido hudu da shugaba Mathieu Kerekou da wakilan majalisar dokoki da kuma na al’adun kasar. A baya ga haka Horst Köhler ya kaddamar da bikin bude wata kasaitacciyar gada, wacce cibiyar rance domin ayyukan sake ginawa ta Jamus ta taimaka wajen ginata a cikin shekaru uku kacal, a birnin Cotonou. A nata bangaren Kerstin Müller, karamar minista a ma’aikatar harkokin wajen Jamus dake wa shugaban rakiya ta rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyin ma’amallar kasa da kasa guda uku, wadanda gaba daya suka kunshi tsabar kudi Euro miliyan 46. A lokacin da take bayani karamar ministar tayi nuni da irin ci gaban da kasar Benin ta samu a cikin 'yan tsirarun shekarun da suka wuce wajen farfado da tattalin arzikinta kuma a saboda haka kasar ta cancanci samun cikakken goyan baya akan manufa.