Shugaban kasar Isra´ila ya rushe majalisar dokoki | Labarai | DW | 23.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban kasar Isra´ila ya rushe majalisar dokoki

Shugaban kasar Israela Moshe Katsav, a yau laraba, ya sa hannu a kann dokar rushe majalisar dokokin Knesset, tare da kiran zaben yan majalisun dokoki ranar 28 ga watan maris na shekara mai zuwa.

Katsav ya dauki wannan mataki bayan murabus din da Ariel Sharon yayi, daga jam´iyar sa ta Likud, da kuma mukamin sa na Pramista a shekaran jiya.

Tunni, har tsofan Praministan, ya kirkiro wata sabuwar jam´iya da ta samu tabaraki, daga shugaban kasa.

Masu kulla da al´ammuran siyasa a Israla, na jera wannan sabuwar jam´iya a kunnan doki, da jam´iyar kwadago, a yayin da jam´iyar Likud ke rike da matsayi na 3.

Ariel Sharon ya zuwa yanzu ya samu goyan nbaya daga yan majalisar dokoki 15 na jam´iyar Likud, da wasu gagga a fahgen siyasar Isra´ila.

Kazalika, ya shiga tantanawa da tsofan Praminista Shimon Perez, na jam´iyar Kwadago, wanda bisa dukkan alamu, zai yi murabus daga jam´iýar sa kamin zaben, domin kulla kawance da Sharon.