Shugaban kasar Iran ya soki lamirin Amurka da Britaniya | Labarai | DW | 26.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban kasar Iran ya soki lamirin Amurka da Britaniya

Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmedinejad ya soki lamirin kasashen Amurka da Britaniya dangane da tashin wasu bama bamai biyu da suka yi sanadiyar mutuwar mutane shidda a kudu maso gabashin birnin Ahvaz a can kasar Iran. An ruwaito shugaban na Iran na cewa alhakin wannan hari ya taállaka ga kasashen biyu na Amurka da kuma Britaniya. Bugu da kari shugaban ya umarci ministan harkokin wajen kasar ya kaddamar da bincike domin gano hasashen da ake na kasancewar hannun wasu yan kasashen ketare a harin bom din da ya auku. An baiyana yawaitar tashin tarzoma a tsakanin jinsin larabawa mazauna lardin Ahvaz . A yan watannin da suka gabata, kasar Iran ta zargi Britaniya da hadasa tarzoma a yankin wanda ke kan iyaka da kasar Iraqi inda Britaniyan ke da sansani soji kimanin 8,500. Tuni dai gwamnatin Britaniyan ta musanta zargin cewa tana da hannu a wannan hari.