Shugaban kasar Iran ya aika da wasika ga shugaban Amurka | Labarai | DW | 08.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban kasar Iran ya aika da wasika ga shugaban Amurka

Shugaban kasar Iran Mahmud Ahmedinajad,ya aike da wasika ga shugaba Bush na Amurka,yana mai shawarta sabbin hanyoyi da zasu bi su sasanta banbance banbance dake tsakaninsu.

Wannan itace takarda ta farko da wani shugaban kasar Iran zai aikewa shugaban Amurka cikin shekaru 27.

Kakakin maaikatar Hamid reza ya fadawa kanfanin dillancin labarai na AP cewa,ministan harkokin waje Manucher Muttaki,ya mika takardar ga jakadan kasar Switzerland.

Ofishin jakadancin na kasar switzerland yana da sashe dake kula da alamuran Amurka.

Kakakin maaikatar bai baiyanawa yan jarida abinda takardar ta kunsa ba,amma yace sabbin shwarawari ne da zasu magance matsalolin kasa da kasa,da kuma halin da ake ciki a duniya.