Shugaban kasar Faransa Jacques Chirac ya sha alwashin magance matsalolin da suka haddasa tarzoma a kasar. | Labarai | DW | 15.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban kasar Faransa Jacques Chirac ya sha alwashin magance matsalolin da suka haddasa tarzoma a kasar.

Shugaban kasar Faransa Jacques ya yiwa alúmar kasar wani muhimmin jawabi a karon farko tun bayan barkewar rigingimu da suka dabaibaye kasar a kusan makwanni uku. Jacques Chirac ya sha alwashin tabbatar da doka da oda yana mai cewa tarzomar dake faruwa a tsawon kowane dare na yin barazana ga kyakyawan tsarin kasar Faransa na rungumar baki da shigar da su cikin alámura na yau da kullum. Bugu da kari ya yi alkawarin daukar managartan matakai na magance manyan matsalolin da suka haddasa tarzomar. Yace zai kafa wata hukuma da zata taimakawa matasa samun aikin yi. A halin da ake ciki kuma majalisar zartarwar Faransan ta tsawaita dokar ta baci da aka sanya a wasu lardunan kasar a makon da ya gabata. A yau ne majalisar dokokin kasar zata yi muhawara don amincewa da karin waádin dokar ta bacin ta tsawon watanni uku.