Shugaban kasar Brazil ya fara ziyara aiki a nahiyar Afrika | Labarai | DW | 07.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban kasar Brazil ya fara ziyara aiki a nahiyar Afrika

Yau ne shugagan kasar Brazil, Luiz Inacio Lula Dasylva, ya fara rangadi a kasashen Afrika.

Wannan ziyara da itace irin ta ta 5 ,da shugaban Brazil ,ya kai Afrika, na dauke da burin samun hadin kan wannan kasashe, ta fannin shirya wata gagaramar haduwa, tsakanin kasashe masu tasowa da masu arzikin masana´antu, da zumar warware kikikakar da ake fuskanta a huldodin cude ni in cude ka a tsakanin su.

Lula Dasylva, zai ziyarci Algeria, Benin, Bostwana, da Afrika ta kudu, inda zai halarci wani babban taro,. Ranar ladi mai zuwa, a game da batun sallon mulkin demokradiya.

Kazalika zai anfani da wannan dama,domin rattaba hannu a kan yarjeniyoyi da dama, ta fannin kiwon lahia, kasuwanci, da kuma ilimi.