Shugaban Karzai ya katse jawabi a filin wasa na birnin Kabul | Labarai | DW | 09.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Karzai ya katse jawabi a filin wasa na birnin Kabul

Shugaban Afghanistan Hamid Karzai ya sake yiwa ´yan tawayen Taliban tayin tattauna batun zaman lafiya. A lokaci daya shugaban ya nunar a fili cewa akwai matsaloli dangane da tuntubar kungiyar ta masu tsattsauran ra´ayi. Da farko dai shugaba Karzai ya katse jawabin da yake yi a wani filin wasa dake birnin Kabul sakamakon wani hargitsi da aka samu a wajen filin wasan. Masu tsaro lafiyar sa sun kare shi. Wasu mutane suka yi kokarin kutsawa cikin filin wasan da karfin tuwo, inda shugaba Karzai ke yiwa wasu mutane kimanin dubu 25 jawabi. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce ´yan sanda sun yi harbi cikin iska don tarwatsa gungun mutane amma ba wanda ya jikata. A shekarun baya dai shugaba Karzai dai ya sha tsallake rijiya da baya a yunkurin halaka shi.