Shugaban Jibuti ya sake lashen zabe | Labarai | DW | 09.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Jibuti ya sake lashen zabe

Shugaba Omar Guelleh na Jibuti da ya shafe shekaru 17 kan madafun iko ya sake lashe zabe.

Shugaba Omar Guelleh na kasar Jibuti ya sake lashen zaben shugaban kasar da ya gudana a wannan Jumma'a da ta gabata, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar. Shugaban ya shafe shekaru 17 kan madafun iko.

Akwai 'yan takara shida da suka fafata neman shugabancin kasar wadda Faransa ta yi wa mulkin mallaka da ke yankin kahon Afirka. Firaminista na Abdoulkader Kamil Mohamed kasar ya bayyana a kafofin yada labarai na gwamnatin inda ya bayar da tabbacin cewa Shugaba Omar Guelleh ya lashe zaben a zagayen farko.