Shugaban Jamus Köhler ya fara ziyarar aiki ta yini huɗu a Ghana | Labarai | DW | 11.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Jamus Köhler ya fara ziyarar aiki ta yini huɗu a Ghana

Shugaban Jamus Horst Köhler ya isa a Accra babban birnin kasar Ghana a farkon wata ziyarar aiki ta yini hudu wadda a ciki zai gana da shugaba John Kuffour. Köhler zai kuma halarci babban taro karo na biyu na wani shiri da ya kirkiro na dangantaka da nahiyar Afirka. Daga gobe wato 12 zuwa 14 ga watan nan na janeru za´a gudanar da taron a birnin Accra mai taken yankuna biyu amma makoma guda. Babban taron wanda ya hada shugabannin siyasa da mayan ´yan kasuwa da masu binciken kimiyya da na al´adu daga kasashe 30, zai mayar da hankali akan hanyoyin da za´a bi wajen inganta hadin kai da dangantaku tsakanin Afirka da kasashe masu ci-gaban masana´antu.