1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Jamus Horst Köhler yayi kira da a samar da zaman lafiya a GTT

Shugaban tarayyar Jamus Horst Köhler yayi kira ga Isra´ila da Falasdinawa da su hanzarta samar da zaman lafiya tsakaninsu. A jawabin sa n bude taron yini biyu na tuntubar juna tsakanin Turai da Isra´ila a birnin Berlin shugaba Köhler yayi kira ga Amirka da kuma nahiyar Turai da su dauki kwararan matakan ciyar da shirin wanzar da zaman lafiyar yankin Gabas Ta Tsakiya gaba. Köhler ya ce ko da yake wajibi ne Isra´ilawa su samu ´yancin tafiyar da rayuwarsu a ko-ina cikin duniya ba tare da wata fargaba ba, amma su ma Falasdinawa na da ´yancin samun kasar kansu mai karfi a fannin siyasa da na tattalin arziki.