Shugaban Jammiiyyar Adawa na APC ya lashe zaben Saleon | Labarai | DW | 17.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Jammiiyyar Adawa na APC ya lashe zaben Saleon

Humukamar zaben kasar Saleon,ta sanarda Shugaban jammiiyyar adawa Ernest Bai Koroma amatsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.Sanarwar data fito daga hukumar zaben na nuni dacewa shugaban jammiyyar adawn na APC,ya samu nasara ne da kuriu kashi 54.6 daga cikin 100,na adadin kuriu da aka kada a zaben zagaye na biyun shugaban kasa,daya gudana a ranar 8 ga wanna wata na satumba,ayayinda abokin takararsa kuma mataimakin shugaban kasa Solomon Berewa na jammiiyar dake mulkin Saleon ,ta SLPP ya samu kashi 45.4 daga cikin yawan kuriun da aka kada.

Wannan sanarwa ta hukumar zaben Saleon din dai,tazo ne ,bayan da jammiiyyar data sha kaye kuma mai mulki a yanzu,.tayi barazanar zuwa gaban kotu domin kalubalantar sakamakon zaben ,saboda rashin sahihancinsa.