1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Jammeh na kan gaba a zaben kasar Gambia

Sakamakon farko da aka samu na zaben shugaban kasar Gambia da aka gudanar jiya ya yi nuni da cwea shugaba Yahya Jammeh ke kan gaba. Alkalumman da hukumar zaben kasar ta bayar sun ce shugaba Jammeh ya yi nasara a mazabu 12 daga cikin 48 da kawo yanzu aka kammala kidayar kuri´unsu. Shugaban ´yan adawa Oussainou Draboe na matsayi na biyu. Hukumar ta ce a wani lokaci a karshen wannan mako za´a samu cikakken samakamkon zaben, wanda rahotanni suka ce ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana.