Shugaban jam´iyar Liberal Democrats a Birtaniya yayi murabus | Labarai | DW | 07.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban jam´iyar Liberal Democrats a Birtaniya yayi murabus

Shugaban jam´iyar Liberal Democrat ta masu sassaucin ra´ayi a Birtaniya wato Charles Kennedy ya yi murabus sakamakon matsin lambar da ya yi ta sha daga ´ya´yan jam´iyar. Mista Kennedy ya ce ya dauki wannan mataki don hadin kan jam´iyar. Sama da rabin wakilan jam´iyar a majalisar dokoki suka yi kira gare shi da yayi murabus, bayan ya fito bainar jama´a ya amsa cewar ya yi fama da matsalar shan barasa. A lokacin daya Kenneddy mai shekaru 46 da haihuwa ya ba da sanarwar gudanar da sabon zaben shugabannin jam´iyar.