Shugaban jam´iyar CSU ya ce ba zai shiga cikin gwamnatin kawance ba | Labarai | DW | 01.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban jam´iyar CSU ya ce ba zai shiga cikin gwamnatin kawance ba

Shugaban daya daga cikin manyan jam´iyun ´yan ra´ayin mazan jiya a nan Jamus, Edmund Stoiber ya ce ba zai shiga cikin gwamnatin hadin guiwa tsakanin CDU´/CSU da SPD a karkashin Angela Merkel ba. Rahotanni sun ce Stoiber wanda shine shugaban jam´iyar CSU ya yanke shawarar ci-gaba da zama jihar Bavariya a matsayin Firimiyan wannan jiha maimakon ya tare birnin Berlin a matsayin ministan tattalin arziki a karkashin gwamnatin Merkel, shugabar jam´iyar CDU. In an jima kadan ne Stoiber zai ba da wata sanarwa a bainar jama´a game da wannan shawara da ya yanke. A jiya daddare Stoiber ya fadawa manema labarai cewa yana shakkar shiga cikin wata babbar gwamnatin kawance da jam´iyar social democrat bayan da shugabanta Franz Müntefering ya sauka daga wannan mukami.