Shugaban Iran ya kai ziyara farko a Haɗɗaɗiyar Daular Larabawa | Labarai | DW | 13.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Iran ya kai ziyara farko a Haɗɗaɗiyar Daular Larabawa

Yau ne shugaba Mahamud Ahmadinejad na Iran, ya ga gana da takwaran sa, mai Martaba Sarki Cheick Khalifa Ben Zayed Al-Nahyane, na haɗɗaɗiyar Daular Laraba.

Wannan itace ziyara farko da wani shugaban ƙasar Iran ya taba kaiwa a wannan ƙasa, mussamman domin tantana batun zaman lahia, tsakanin a yankin Golf.

Ahmadu Nidjad, da sarki Check Khalifa, sun yi mahaurori a game da halin da ake cikin,a fagen siyasar dunia.

A dangane da batun makaman nuklea, Ƙasashen yankin Golf, sun bayyana adawa da matakin Iran na mallakar makaman ƙare dangi, to saidai kuma, a ɗaya hannun su na adawa a game da manufofin Amurika na ƙaddamar da yaƙi ga Iran.

Hukumomin Dubai da na Teheren, sun yi anfani da wannan dama, inda su ka tantana matsalolin iyakokin su na ruwa, da kuma sauran batutuwa da su ka shafi tattalin arziki.

Gobe idan Allah ya kai mu,Mahamud Ahmadinedjad, zai kawo ƙarshen ziyara, tare da kiran taron manema labarai.