1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Iran Ahmedinejad ya isa a birnin New York

September 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuAO
A daidai lokacin da ake fama hauhawar tsamari tsakanin Amirka da hukumomin Teheran, shugaban Iran Mahmud Ahmedi-Nejad ya isa a birnin New York inda zai halarci babban taron MDD. Goron gayyatar da aka ba sa na yin jawabi a jami´ar Colombia ya janyo kace-nace. Wasu ´yan siyasa a Amirka da kungiyoyin addinai da na Yahudawa sun yi tir da wannan gaiyata, to amma shugaban jami´ar na Colombia Lee Bollinger ya ce babu gudu babu ja da baya inda ya nuni da ´yancin fadar albarkacin baki. Daruruwan mutane dai sun yi gangami a gaban hedkwatar MDD da kuma jami´ar ta Colombia don yin tir da ziyarar ta Ahmedi-Nejad. A kuma halin da ake ciki Iran ta rufe kan iyakokin ta da arewacin kasar Iraqi don nuna adawa da kamun wani dan Iran da sojojin Amirka suka yi.