Shugaban Iran Ahmedinejad ya fara ziyararsa ta farko a Afghanistan | Labarai | DW | 14.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Iran Ahmedinejad ya fara ziyararsa ta farko a Afghanistan

Shugaban Iran Mahmud Ahmedi-Nijad ya yi watsi da zargin da Amirka da Birtaniya ke yi cewa Iran na tura makamai ga mayakan Taliban wadanda ke yakar gwamnatin Afghanistan da dakarun kasa da kasa. Shugaba Ahmedi-Nijad ya nunar da haka ne a gunw ani taron manema labarai da suka yi da shugaban Afghanistan Hamid Karzai a birnin Kabul, a ziyarar sa ta farko zuwa wannan kasa tun bayan darewarsa kan kujerar shugaban Iran. Ya ce kasarsa na marawa dukkan shirye shiryen girke sahihiyar demukiradiyya a Afghanistan baya. Shugaban na Iran ya nanata cewa dole ne kasashen biyu su karfafa hadin kai a fannonin tsasro da raya kasa. Jami´an Birtaniya da Amirka dai na zargin cewa ana taimakawa ´yan tawayen Taliban da makamai kirar Iran a yakin da suke yi da gwamnatin Kabul da kuma dakarun kasa da kasa a Afghanistan.