Shugaban Iran Ahmedinejad ya fara ziyarar aiki a Belarus | Labarai | DW | 21.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Iran Ahmedinejad ya fara ziyarar aiki a Belarus

Shugaban Iran Mahmud Ahmedi-Nijad ya sauka a Minsk babban birnin kasar Belarus inda zai fara wata ziyarar aiki ta yini biyu. Kamar yadda gwamnati a birnin na Minsk ta nunar manufar wannan ziyara ita ce sanya hannu kan yarjeniyoyin hadin kan tattalin arziki tsakanin Iran da Belarus. Bugu da kari a tattaunawar da zasu yi, Ahmedinijad da takwaransa na Belarus Alexander Lukashenko zasu mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi makamashi, ciniki da kuma kimiyya. Shugaba Lukashenko wanda kasashen yamma suka mayar da shi saniyar ware ya sha yabawa da kyawawan dangantaku tsakanin kasar sa da Iran. Ana zargin gwamnatin sa da sayarwa Iran makamai kirar Rasha.