MDD ta bukaci Turai kan tsari mai kyau ga 'yan gudun hijrah
September 14, 2015Talla
A yayin bude taron hukumar karo na 30 a birnin Geneva Shugaban hukumar kare hakkokin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra'ad Al Hussein ya jaddada kudirin hukumar na ganin mahukuntan Afirka da Amirka da yankin Asiya gami da nahiyar Turai daukar kwararan matakai masu inganci domin jin dadin 'yan gudun hijira a duniya.
Kazalika Zeid Ra'ad ya kuma jinjina wa masu zanga-zangar nuna goyan bayan 'yan gudun hijira daga sassan kasashen Tarayyar Turai a bisa yadda suka yi tsayin daka kan halin da 'yan gudun hijirar suka shiga.
Fiye dai da mutane dubu 430,000 'yan gudun hijira da suka ketara zuwa kasashen Turai a wannan shekarar wanda mafi yawancinsu sun fito daga kasashen Larabawa da kuma Afirka.