Shugaban hukumar CIA Goss yayi ajiye aikin sa | Labarai | DW | 06.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban hukumar CIA Goss yayi ajiye aikin sa

Shugaban hukumar leken asirin Amirka Porter Goss yayi murabus ba ba zata, kasa da shekaru biyu bayan ya samu wannan mukami. Ko da yake Shugaban Amirka GWB bai yi bayani game da murabus din da Goss yayi ba, amma ya yaba masa dangane da shawarwari masu fa´ida da yabawa shugaban. Masu lura da al´amuran da ka je ya dawo sun ce watakila jayayya da aka shafe makonni ana yi tsakanin Goss da John Negroponte ta sa Goss din ya ajiye aikinsa. Goss ya ce ya tuntubi shugaba Bush kafin ya yanke wannan shawara. Goss ya karbi mukamin shugaban hukumar CIA ne da nufin yi mata kwaskwarima bayan wasu kurakurai na leken asiri da aka tabka bayan hare haren 11 ga watan satumban shekara ta 2001 da kuma yakin kasar Iraqi. Har yanzu dai ba´a san wanda zai maye gurbisa ba.