1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban gwamnatin tarayar Jamus na ci gaba da ziyararta ta farko a Isra’ila.

January 30, 2006
https://p.dw.com/p/BvAG

A ziyarar da take kaiwa a Isra’ila, shugaban gwamnatin tarayyar Jamus, Angela Merkel, ta yi kira ga shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas da ya shawo kan kungiyar nan ta Hamas ta amince da Isra’ila, sa’annan kuma ta kauce daga duk wasu tashe-tashen hankulla. Da take yi wa maneman labarai jawabi bayan ganawarta da shugaban kasar Isra’ilan, Moshe Katsav yau a birnin kudus, Angela Merkel ta ce Abbas na da wani babban nauyi da ya rataya a wuyarsa. A yau din ne kuma ake sa ran Merkel za ta sadu da shugaban Falasdinawan mai barin gado Mahmoud Abbas a birnin Ramallah. Rahotanni dai sun ce shugaban ta Jamus, ba za ta gana da da `yan kungiyar Hamas din ba, a wannan ziyarar tata, wadda ita ce ta farko a yankin tun da ta hau karagar mulki.

Da take jawabi game da nasarar da kungiyar Hamas ta samu a zaben hukumar Falasdinawan, jim kadan bayan saukarta jiya a Isra’ilan, Angela Merkel, ta yi barazanar katse duk wani taimakon kungiyar Hadin Kan Turai ga Falasdinawan, idan Hamas ba ta canza matsayinta game da kasar bani Yahudun ba.