Shugaban Guniea Lansana Conte ya naɗa Eugene Camara a mukamin Firaminista | Labarai | DW | 10.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Guniea Lansana Conte ya naɗa Eugene Camara a mukamin Firaminista

Jim kadan gabanin cikar wani wa´adi na ´yan adawa shugaban kasar Guinea Lansana Conte ya nada sabon FM. Yanzu haka dai tsohon ministan batutuwan da suka shafi ayyukan shugaban kasa Eugene Camara zai karbi mukamin FM. To amma ´yan adawa na zargin cewa Camara na hannun damar shugaban kasar ne saboda haia ba zai iya yanke wata shawara da kan shi ba. da farko ´yan adawan sun bawa shugaban wa´adin zuwa gobe lahadi da nada sabon FM. A cikin watan afrilun bara shugaba Conte ya sallami tsohon FM Cellou Diallo, sannan tun daga wannan lokaci ba´a nada sabo ba. Tun a shekara 1984 Conte ya dare kan kujerar shugaban kasar ta Guinea.