1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Guinea na fuskantar tuhuma kan rashawa

Ramatu Garba Baba
May 4, 2018

Shugaban kasar Guinea Alpha Conde zai shigar da kara bisa zargin ba ta ma sa suna biyo bayan bincike da Faransa ta kaddamar kan kamfanin Bollore da ke aikin gina hanyoyi na jiragen kasa a kasashen yammancin Afirka.

https://p.dw.com/p/2xBJM
Alpha Conde
Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Alpha Conde ya ce zai shigar da kara don ganin an wanke shi daga wannan zargin, ya kuma ce a shirye ya ke ya amsa kiran bangaren adawa da suka nemi a soma bincikensa kan batun. Wannan na zuwa ne bayan da a watan da ya gabata, hukumomin kasar Faransa suka kama, tare da tsare attajirin dan kwangilan Vincent Bollore bisa zargin da ake yi masa na bayar da cin hancin ga shugabani.

Tashoshin jiragen ruwa wanda kamfanin Bollore ya gina a kasashen yammacin Afirka, da suka hada da kasar Togo da Guinea da kuma Cote divoire na daga cikin wadanda aka gano ya samu kwangiloli ne bayan kamfanin ya bayar da na goro, abinda alkalai a Faransa ke kokarin tantacewa. Gwamnatin kasar Togo ma ta ce a shirya ta ke ta bada hadin kai ga Faransa idan bukatar hakan ta taso a shari'ar.