Shugaban Guinea Lansana Conte yayi kira da hadan kan kasa | Labarai | DW | 21.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Guinea Lansana Conte yayi kira da hadan kan kasa

A dangane da yajin aikin gama gari da kuma mummunar arangama da ake yi a Guinea, shugaba Lansana Conte yayi kira da hadin kan kasar baki daya. A cikin wani jawabi ta gidan radiyo shugaban yayi kira ga al´umar kasar da kuma soji da su marawa gwamnatins a baya. Kimanin kwanaki 12 da suka wuce shugabannin kwadago suka kira yajin aiki na gama gari da nufin matsawa shugaba Conte mai fama da rashin lafiya lamba, da ya sauka. Tun daga sannan an yi ta arangama tsakanin masu zanga-zangar kyamar gwamnati da jami´an tsaro, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 10.